Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta
cewa, ya nakalto da shafin Ramallah A lokacin da yake zantawa da manema labarai
a jiya a babbar cibiyar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar, babban
malamin cibiyar Ahmad Tayyib, ya bayyana abin da ya faru na kai hari kan
musulmi da taka su da mota bayan kammala salla a birnin London da cewa, wannan
aiki ne da ya cancanci Allah wadai daga dukkanin al'ummomin duniya.
Ya ce suna kiran gwamnatin Birtaniya da ta dauki dukkanin matakan da ska dace domin baiwa musulmi kariya, domin kaucewa sake faruwar irin wannan aiki na keta alfrmar addini da 'yan adamtaka, da nuna bangaranci ga wani jinsi na al'ummar kasar ta Birtaniya saboda akidarsu ta addini.
Daga karshe kuma ya kirayi musulmin Birtaniya da su ci gaba da zaman lafiya da sauran jama'a tare da kyautatawa kamar yadda musulunci ya yi umarni, haka nan kuma kada su bari ayyukan wawaye su tunzura su domin aikata abin dace da su ba.