Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga
shafin jaridar Anha cewa, wani dan kasar saudiyya ya gano wani kwafin kur'ani a
masallacin asibitin gwamnati a yankin Jubail a gabashin Saudiyya wanda yak
edauke da kure wajen bugu.
Bayanin y ace wannan kur'ani an gano kura-kurai a cikin shafukansa guda uku, daga suka hada da faraway da surat mudassir a matsayin surat fatiha.
Ahmad Jarrah shugaban cibiyar kula da harkokin addini a yankin Jubail ya bayyana cewa, sun kwace wanann kur'ani, kuma suna gudanar da bincike a kan sauran kwafin da aka buga su tare da shi a madaba'antar sarki fahad da ke buga kur'ani domin hana aiki da su.