Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin yanar gizo na kamfanin dillancin labaran express cewa, da jiffifin safiyar jiya wani mutum a cikin wata babbar mota yay i nufin kai hari a kan musulmi bayan kammala sallar asuba a garin carty.
Jami’an tsaro sun kame mutumin a lokacin da yake ‘yan mitoci tsakaninsa da masallacin, inda suka hana shi iya a kan musulmi da suke fitowa daga masallaci.
Jami’an ‘yan sandan faransa sun ce yunkurin kaddamar da harin yana da alaka ne da kyamar musulmi a kasar.
Bayan kame mutumin ya bayyana cewa, yana da nufin daukar fansa ne kan hare-haren da ‘yan daesh suka kaddamar a shekarar da ta gabata a birnin Paris.
‘Yan sanda sun ce suna gudanar da bincike kan lamarin, amma za a ci gaba da tsdare mutumin a hannn hukuma kafin gurfanar da shi a gaban kuliya.
Akwai muuslmi kusan miliyan biyar a kasar Faransa, kamar yadda kuma akwai masallatai kianin 2500 a sassa daban-daban na fadin kasar.