Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga bangaren hulda da jama’a na ma’aikatar yada al’adun muslunci cewa, an gidanar da wannan baje koli ne a birnin Pretoria fadar mulkin kasar firka ta kudu wanda ofishin kula da harkokin al’adun musulunci na Iran ya dauki nauyin shiryawa.
Wannan baje koli dai ya nuna wasu daga cikin ayyuka na nau’oin fasaha irin na masana fasahar rubutun kur’ani na kasar Iran, wadanda aka rubuta ko dai a kan manyan allula ko kuma a kan takardu ko littfai.
Wannan baje koli dai ya samu halartar masana daga sassa daban-daban na kasar da suka hada da musulmi da ma wadanda ba musulmi ba, domin ganin irin wannan fasaha ta muslunci mai kayatarwa.
Baya ga baje kolin, wasu daga cikin masu ayyukan fasahar sun bude wani aji a wurin na koyar da irin wannan aikin fasaha ga masu bukatar koyo ko kuma samun masanai a kan yadda ake gudanar da shi.