IQNA

Adadin Musulmi Masu Zuwa Amurka Ya Ragu

23:57 - July 13, 2017
Lambar Labari: 3481697
Bangaren kasa da kasa, sakamakon wani bincike ya nuna cewa adadin musulmi masu yin hijira zuwa Amurka ya ragu matuka a cikin watanni biyar da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na usatoday cewa, sakamakon binciken da cibiyar bincike ta pio ta gudanar a kasar Amurka, ta tabbatar da cewa, mutanen da suka yi hijira zuwa Amurka cikin watanni biyar ad suka gabata kimanin 50% daga cikinsu mabiya addinin kirista ne, yayin da adadin musulmi bai wuce kashi 38 ba.

Bayanin ya ce wannan lamarin ya faru ne tun bayan hawan Donald Trumpa kan kujerar shugabancin Amurka, da kuma tasirin barazanar da yake yi a kan msuulmi tare da nuna musu kyama, inda akasarin wadanda suka shiga kasar daga cikin musulmi ‘yan kasar Syria ne.

Bayan ‘yan Syria kuma sai ‘yan kasashen Afghanistan da kuma Somalia, wadanda su ne suka fi samun damar shiga kasar sakamakon matsalolin da suke fama da sua cikin kasashensu.

Tun a lokacin yakin neman zabe Dpnald Trump ya bayyana matsayinsa a kan msuulmi, wanda kuma sakamakon hakan ne kin jinin musulmi ya karu a kasar a hukuamnce, kamar yadda kuma ya kafa dokar hana muslmi shiga kasar daga wasu kasashe.

3618497


captcha