Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shugaban ofishin kula da harkokin al’dun musulunci na kasar Iran a Senegal Sayyid Hassan Esmati ya mika kyautar kwafin kur’ani mai tsarki tarjamar harshen faransanci ga babban daraktan radiyon Doflanga kasar Senegal Dawud Jouf.
Bayanin ya ce Esmati ya halarci wanann gidan radiyo mai dimbin masu saurare da ke kasar Senegal inda ya ga irin shirin da ake gudaarwa, musamman ma dai a bangaren addini, ya kuma yaba da yadda masu aiki a wurin ke yin aiki tukuru domin wayar da kan jama’a kan lamurra da dama da suka shafi addini da zamantakewa.
Wannan yana da cikin muhimman ayyuka da ofishin kula da harkokin al’adu na kasar Iran ke gudanarwa adukaknin kasashen musulmi, domin tabbatar da cewa sakon juyin islama ya isa ga al’ummomin musulmi.