Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tun bayan harin daukar fansa a kan jami'an tsaron yahudawan Isra'ila da wasu Palastinawa 'yan gwagwarmaya suka kai a kusa da kofar masallacin Quds a ranar Juma'a da ta gabata, har yanzu yahudawan na ci gaba da rufe masallacin mai alfarma.
Harin wanda ya yi sanadiyyar halakar 2 daga cikin sojojin yahudawa tare da yin shahadar maharan uku, ya girgiza haramtacciyar kasar Isra'ila matuka, inda take kallon hakan a matsayin wata manuniya kan cewa, Palastinawa sun fara daukar wasu sabbin matakai na daukar fansa kan kisan da ake yi musu a kullum rana ta Allah.
Kungiyoyin gwagwarmaya na Palastinawa da kuma wasu kasashen larabawa da suka hada da Lebanon, sun yi na'am da wannan harin daukar fansa a kan jami'an tsaron yahudawan Isra'ila.