Kamfanin dilalncin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa Muhyiddin Afifi babban sakatare kwamitin kula da kuma sanya ido a kan harkokin buga kur'ani a kasar Masar da ke karkashin cibiyar Azhar ya bayyana cewa, kwamitin nasua shirye yake ya dauki sabbin mambobi da za su yi a cikin kwamitin.
Ya ci gaba da cewa an dauki wannan mataki ne domin bayar da dama ga masana da za su iya bayar da gudunmawa wajen tantance ayyukan da ake gudanarwa a bangaren uga kur'ani da kuma watsa shia tsakanin al'ummar msuulmi a ciki da wajen kasar ta Masar.
Babban abin da yasa wannan cibiya take kara kaimi wajen kara fadada ayyukanta shi ne, domin tababtar ad cewa an kauce wa buga kur'ania cikin kure, ta yadda masana da dama za su iya dubuwa su bayar da mahangarsu kafin buga ko fitar da kur'ani daga madabanta.
Kafin zama mamba a wannan kwamiti dai sai an bayar da jarawaba wadda malamai zasu shirya, bayan samun makin da ake bukata ne za a iya daukar mutuma matsayin mamba.