Ibrahim Abdullahi shi ne shugaban kungiyar, ya bayyana wannan hari da cewa na ta'addanci ne kuma na dabbanci, domin kuwa babu wani dalili da zai sanya dan adam ya kai haria kan wurin da mutane suke gudanar da ibada ta addininsu.
Ya ci gaba da cewa kungiyarsu wadda take sanya ido a kan lamurra da suka shafi musulmi a Najeriya tana yin Allah wadai da kakkausar muryka wannan mummunan aiki na kai hari a kan coci a kan mabiya addinin kirista.
A bangare guda kuma ya yi kira ga mahukunta da adauki matakin bincike domin gano wadanda suke da ahnnu a cikin wannan aika-aika domin hikunta a gaban kuliya, tare da daukar dukkanin matakan da suka dace domin kare rayukan 'yan Najeriya.
Haka na kuam ya yi kira ga sauran dukkanin mabiya addinai a kasar da su rungumi hakuri da zaman lafiya da juna tare da fahitar juna da kuma girmama ra'ayoyi da akidun junasu a matsayinsu na 'yan kasa guda.