Wannan mataki na zalunci da danniya na iyalan gidan saud ya zo a daidai lokacin da masarutar kasar ta dauki salon shelanta yaki a kan mabiya tafarkin ahlul bait a fadin gabas ta tsakiya.
An kasha mutane da dama tare da jikata wasu da kuma rusa daruruwan gidajen jama'a a yankin an Awamiyya, tare da wawushe dukiyoyin al'ummar yankin wadanda 'yan kasa ne kamar yadda Al Saud suke.
Al ummar gabashin saudiyya mabiya mazhabar shi'a ne wadanda mabiya adidar wahabiyanci suke tsananin gaba da su, wanda kuam masarautar 'ya'yan saud ta ginu ne kan akidar wahabiyanci da yaki da shi'a da kuma 'yan sunna da suke sabawa wannan akida.
Dukkanin arzikin danyen man fetur da iskar gas da Saudiyya ta dogara da shi ana fitar da shi ne daga yankuna 'yan shi'a da ke gabashin kasar, amma kuma ana haramta musu hakkokinsu a matsayinsu na 'yan kasa