Muahhamd Bajuda shi ne shugaban kula da wannan aiki, ya bayyana cewa suna yin hakan ne da nufin ganin ba a samu wata matsala ba, domin kuwa bisa ga al'ada masu gudanar da aikin hajjin suna zuwa wanannwuri mai tsarki a cikin shauki, inda suka taba kyallen ko shafawa, ganin cewa mutane da dama ne a wurin za a iya yaga shi , saboda haka dole ne a daki matakin kaucewa faruwar hakan.