Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga
shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Almasirah cewa, fararen hula da dama ne suka rasa rayukansu da suka hada da
mata da kananan yara wasu da dama kuma suka jikkata, a hare-haren da jiragen
yakin masarautar Al Saud suka kaddamar a yau ranar farko ta wata mai alfarma na
Zul Hijjah, a kan birnin san'a na kasar Yemen.
Rahotannin farko dai na cewa jami'an bayar da agajin gaggawa sun isa wurin domin fitar da gawwaki da kuma kokarin ceto wadanda suka jikkata.
Haka nan kuma rahotannin sun ce akwai yiwuwar adadin yaku bisa la'akari da cewa akwai wadanda suke cikin mawuyacin hali.