IQNA

Kawo Karshen Horar Da Matasa Dubu Daya Karatun Kur'ani A Bagdad

21:25 - August 25, 2017
Lambar Labari: 3481832
Bangaren kasa da kasa, an kawo karshen wani horo da ake baiwa matasa dubu daya na koyar da su karatun kur'ani mai tsarki bisa kaidoji da hukunce-hukuncensa a Bagdad.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin bangaren hulda da jama'a na cibiyar kur'ani da ke karkashin hubbaren Hussaini, cewa, an kawo karshen wannan horo ne wanda matasa kimanin dubu daya suka samu samu horo.

Wannan dai shi ne karon farko da ake gudanar da irin wannan shiri wanda ya gudana a babban masallacin Amirul muminin (AS) da ke birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki.

Shirin dai ya kunshi yara mata da maza dukkaninsu 'yan cikin kasar ta Iraki da suka zo daga larduna da gundumomi daban-daban na kasar.

Ana sa rabn za fada shirin a lokuta masu zuwa, ta yadda zai kunshi yara 'yan kasashen ketare.

3634218


captcha