 Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga
shafin sadarwa na shafaqana cewa, Mariya wadda shekarunta sun kai 104, ta isa
birnin jidda da nufin gudanar aikin hajjin bana.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga
shafin sadarwa na shafaqana cewa, Mariya wadda shekarunta sun kai 104, ta isa
birnin jidda da nufin gudanar aikin hajjin bana.
A lokacin isarta ta samu tarbe daga shugaban karamin ofishin jadancin Indonesia abirnin Jidda da kuma wasu jami'a na gwamnatin saudiyya.
Matar ta nuna farin cikinta maras misiltuwa a lokacin da ta isa birnin na Jidda, inda take ganin lallai Allah madaukakin sarki ya cika mata gurinta na sauke faralin hajji.
Ta ce dukkanin gajiyar da take a cikin jikinta ta fice a lokaci guda bayan isarta birnin na Jidda.