Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta
cewa, kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayar da rahoton cewa,
ita kadai ce 'yar takara da ka mika
sunanta ga kwamitin zaben shugaban kasa, wadda kuma aka amincewa da ita.
Halima Yakub dai ta kasance a majalisar dokokin kasar tun fiye da shekaru ashirin da suka gabata, daga bisani kuma ta zama ita ce shugabar majalisar.
Wannan dai shi ne karon farko da mace musulma ta zama shugabar kasa a wannan kasa da ke gabashin nahiyar asia.
Kasar Singapore mai adadin mutan ekimanin miliyan 5.5, ta samu 'yancin kanta ne shekarar 1965 daga kasar Malaysia.