IQNA

22:48 - September 23, 2017
Lambar Labari: 3481925
Bangaren kasa da kasa, majami’ar mabiya addinin kirista a jahar Massachusetts da ke kasar Amurka za ta shirya wani zaman tattauna kan addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na eagletribune ya habarta cewa, shirin wanda za a fara shi da kimanin karfe 5 na yamma, Robbert Azy ya bayyana cewa, za a gabatar da tambayoyi wadanda musulmi za su amsa dangane da addininsu.

Daga cikin abubuwan da zaman za mayar da hankali a kans akwai batun mahangar addinin mulsuni kan addinin kiristanci da kuma abubuwan da suka hada mahanga ta uslunci da kiristanci.

Baya ga haka kuma akwai abubuwan da ake dangantawa da muslunci wadanda musulmi suke korewa kamar batun ta’addanc, wada musulmi a su bayyana matsayarsu da addinin kan batun ta’addanci da kuma yadda hakan ya sabawa loyarsu, domin masu neman Karin sani kan hakan.

3645067


Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Massachusetts ، Amurka ، musulmi ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: