Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta
cewa, Jagoran ya bayyana haka ne safiyar yau Laraba a lokacinda ya je kusa da
gawar shahid Muhsen Hujaji wanda aka ajiye a masallacin Imam Husain (a) da ke
cikin birnin Tehran. Jagoran ya kara da cewa, shahidai gaba daya suna da babban
matsayin a wajen Allah amma wasun Allah ta'ala yakan daukakasu akan wasu.
Kamar dai yadda muke ganin yadda wannan shihidin ya shiga cikin zukatan ummar
kasar Iran.
A yau Laraba ce za'a zagaya da gawar Shahid Muhsen Hujaji daga Masallacin Imam Husain (a) da ke nan Tehran zuwa dandalin shaheed duk a nan cikin Tehran
Shahid Hujaji ya yi shahada ne a ranar 9 ga watan Agustan da ya gabata a lokacin da mayakan Daesh suka kama shi a kan iyakar kasar Syria da Iraqi a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa hariman Sayyida Zainab dake birnin Demascus na kasar Syria.