Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Independent da ake bugawa a Najeriya tana bayar da rahoton cewa, a jiya musulmi a jahar Ogun da ke tarayyar Najeriya sun bukaci da a bar dalibai mata musulmi da su saka hijabi a cikin yanci a makarantun jahar.
A wani taron da musulmin suka gudanar a wani masallacina birnin Abekuta fadar mulkin jahar sun cimma matsaya kan cewa, wajibi ne mahukuntan jahar su janye duk wata doka a dukkanin makarantu na jahar da ke tilasta mata cire hijabia cikin makarantun.
Wasu daga cikin iyayen yara mata dalibai a wadannan makarantun sun koka a kan cewa an atakura yayansu a makarantu saboda saka hijabin muslunci.
Tajuddin Adeonmi shi ne shugaban kungiyar malamai a jaar ya bayyana cewa, za su gabatar ad wanann bukata ga mahukunta domin daukar matakin da ya dace kan wannan batu, amma dai abin da suke bukata shi ne bayar da dama ga duk mai son saka hijabi ta saka ba tare da tsangwama ba.