Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Sheikh Ali Juma'a mamba a kwamitin manyan malamai kuma tsohon mai bayar da fatawa a kasar Masar ya bayyana cewa abin da ya rage wa Daesh a halin yanzu shi ne shakku kan kur'ani ko kuma karyata shi.
Ya ci gaba da cewa, abin da 'yan ta'addan na daesh suke yi wanda ya ginu a kan akidar wahabiyanci da kafirta msuulmi, ya yi hannun riga da koyarwar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa.
Shehin malamin ya ci gaba da cewa, nauyi ne da ya rataya kan malamai da su ci gaba da wayar da kan musulmi da kuma fadakar da matasa musamman, wadanda su ne suka fi saurin fadawa cikin wannan hatsari na karbar akidar ta'addanci da sunan muslunci.
Kamar yadda kuam ya zama wajibi a ci gaba da yada koyarwar manzo ta hakika, da yin riko da abin da ya koyar a rayuwarsa wanda shi ne addinin msulunci.
Daga cikina bin manzo ya koyar da al'umma kuwa har da tausayi da taimako da kuma son zaman lafiya a tsakanin jama'a, musulmi da wadanda ba msuulmi, domin kuwa yaki yana
zuwa ne matakin kariyar kai.