Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, an buga littafin mai shafuka 123 a cikin harshen Faransanci wanda Sulaiman Sei ya rubuta kuma aka fara sayar da shi a cikin kasar Senegal.
Babban abin da littafin ya kunsa shi ne bin sahihin tafarki na manzon Allah (SAW) wajen bin koyarwarsa da kuma tsarkake ruhi da bautar Allah madaukakin sarki a mahangar Imam Khomeni (RA) da kuma sheikh Ahmadu Bamba Allah ya kara masa rahma, wanda shi ne shi ya assasa darikar Muridiyya a yammacin nahiyar Afirka daga kasar Senegal.
Wannan waliyin Allah sheikh Ahmadu Bamba, wanda ya rasu kusan shekaru dari da suka gabata, ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ilmnatr da jama’a da kuma kwadaitar da su zuwa ga zikirin Allah da ibada, kamar yadda kuma ya yi gwagwarmaya wajen dakushe yunkunrin mulkin mallakar Faransa a Senegal.
Littafin ya hada abubuwa da dama da suke cikin tunaninsa wadanda suka yi daidai da mahangar Imam Khomeini (RA) a bangaren tarbiyar ruhi da zikirin Allah da kuma kusanci zuwa gare shi, bisa dogaro da ayoyin kur’ani mai tsarki.