Kamfanin dillancin labaran iqna ya
habarta cewa, jamar lardin Ziqar a kudancin kasar Iraki suna rigerige wajen gudanar
da ayyukan ciyarwa ga masu tattakin ziyarar Imam Hussain (AS) da ke kan hanya
zuwa Karbala, take da tazarar kilo mita 75 daga yankin.
Daga cikin ayyukan da suka yi har da shimfida wata shimfidar abinci mafi tsawo a tari wadda ta kai taswon kilomitoci, inda masu tattaki sukan tsaya su ci abinci a kan wannan shimfida su wuce.
Wannan dai na daga cikin ayyukan hidima ga masu ziyarar Imam Hussain (AS) da al’ummar wannan lardi suke gudanarwa a kowace shekara.




