Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na kdvr ya habarta cewa, biyo bayan harbin binga da aka yi a cikin majami’ar shugabannin musulmin sun nuna alhininsu ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su.
Iman Jaudah daya daga cikin jagrorin musumi ya bayyana cewa; suna kallon mabiya adinin kirista a matsayin ‘yan uwansu domin kuwa dukkaninsu mutane da suke rayuwa tare a cikin zaman lafiya da fahimtar juna da girmama akidun juna.
A ranar lahadin da ta gabata ce aka kaddamar da hari a kan majami’ar birnin San Antonio da e jahar Texas, inda aka kasha mutane 27 da tare da jikkata wasu 24.
A yayin aukuwar lamarin wani jami’in yan sanda ya rasa rasa, wannan dai bas hi ne karon farko da ake samun wasu masu mummunar aida suna kai hare-hare kan wuraren ibada ba akasar ta Amurka.