Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na qaf ya habarta cewa, an kawo karshen shirin ayyukan kur’ani da aka gudanar a lokacin tattakin arbaeen a ckin larduna daban-daban na kasar Iraki a kan hanyar zuwa birnin karbala mai alfarma.
Muhammad Khalil shi ne babban darakta na shirin kur’ani da ae gudanarwa akan hanyar Karbala a lokacin tarukan zyarar arbaeen, ya bayyana cewa a cikin yardarm Allah wannan shiri y gudana a cikin nasara.
Ya ce fiye da malaman kur’ani dubu ne suka bayar da gudunmawa wajen jagorantar shirin, a kuma kafa wurare 450 a cikin larduna 13 na Iraki a kan hanyar zuwa Karbala.
Daga cikin ayyukan da aka gudanar akwai zaman karatun kur’ani da kyautata tilawa, da kuma koyar da hukunce-hukuncen karatun kur’ani, sai kuma fitar da darussa da suke a cikin ayoyin kur’ani mai tsarki, tare da tafsirin ayoyi.
Abin tuni a nan dai shi ne, wannan shiri ana gudanar da shi tsawon shekaru uku a jere, tare da halartar miliyoyin masu zyara da suke yada zango a wadannan wurare.