Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta
cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na shafaq cewa, babban
sakatare majalisar dinkin duniya ya aike ad sakon ta'aziyya zuwa ga gwamnatoci
da al'ummomin Iraki da Iran, dangane da girgizar kasar da aka yi wadda ta lashe
rayukan jama'a.
Ya ci gaba da cewa hakika abin da ya faru lamari ne nab akin ciki, kuma majalisar dinkin duniya a shirye take ta bayar da dukkanin taimakon da ake bukata.
A daren jiya ne dai aka samu girgizar kasa wadda ta kai daraja 7.3 a ma'aunin ritche a Kermansha da ke Iran da kuma Sulamimaniyya a Iraki.
Haka nan kuma an ji motsin wannan girgizar kasa a kkasashen Turkiya, Armania, saudiyya, Kuwait da kuma hadaddiyar daular larabawa.