IQNA

Limamamin Juma’a A Tehran:
23:48 - December 01, 2017
Lambar Labari: 3482155
Bangaren siyasa, Ayatollah Muwahhidi Keramani wanda ya jagoraci a sallar Juma’a a Tehran ya bayyana cewa, kawar da daular wahabiyawa ta Daesh a Siriya da Iraki ya tabatar da karfin muslunci ne da kuma ran gami da Hizbullah, wadanda suka bayar da gagarumar gudunmawa.
Kawar Da Daular Daesh Ya tabbatar da Karfin Musulunci, Iran da kuma HizbullahKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Limamin da ya jagoranci sallar juma'a na nan birnin tehran ya yi kira ga musulmi sunna da shi'a da suka kama hannuwan juna su fuskanci makiyan al'uumar musulmi, tare da yin tsayin daka da kuma gwagwarmaya.

Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidi Karmani ya yi kira ga musulmi sunna da shi'a da suka kama hannuwan juna su fuskanci makiyan al'uumar musulmi, tare da yin tsayin daka da kuma gwagwarmaya.

Ayatullah Muhammad Ali Muwahhidi Karmani ya kara da cewa; Bai kamata shi'a da sunna su bari makiyan musulunci su yaudare su ba, domin ba su yarda da hadin kai atsakanin musulmi ba.

A yayin da yake ishara kan iyalan gidan anabta tsarkaka ya cesu ne gimshikin hadin kai a tsakanin al'ummar musulmi, ayatollahi kemani ya ce wasu daga hukumomin musulmi sun kasa tabbatar da hadin kai tsakanin al'ummar musulmi saboda sun yaudaru damakircinmakiyan musulimci.

Ayatollahi Kermani ya kara da tabbatar da cewa a halin yanzu karfin marja'iya, kungiyar Hizbullah ya kasar Labnon da Dakarun musulinci da iran ya bayyana a wurin Amurka da duk wasu kasashe masu girman kai na duniya, to amma kada mu gafala da makircin makiya, ya kamata mu zamanto masu basira da ganewa a game da duk wani makirci da makiyan musulinci suke kullawa.

Har ila yauLimamin juma'ar ya yi wa al'ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar manzon Allah (s.a.w.)

3668524

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: