Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Almasira cewa, mayakan kungiyar Ansarullah a kasar Yemen Yemen sun harba makami mai linzami zuwa brnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
Bayanin ya ce wannan mataki yana zuwa ne a matsayin mayar da martini dangane da hare-haren wuce gona da iri da kisan gilla da kawancen da masarautar 'ya'uan gidan Saud ke jagoranta ne kan al'ummar Yemen.
Tun kafin wannan lokacin da mayakan na Yemen sun barazanar mayar da martini kan hadaddiyar daular larabawa, daya daga cikin kasashen ad suke a sahun gaba wajen taimaka 'ya'yan Saud a kisan gillar da suke kan al'ummar Yemen.