IQNA

16:11 - December 14, 2017
Lambar Labari: 3482199
Bangaren kasa da kasa, Sakatare janar na Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) ya bukaci kasashen Duniya da su amince da kasar Palastinu a hukumance.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Yayin da yake jawabi a zauren taron Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) da ya gudana yau laraba a birnin Istambul na kasar Turkiya, Yusuf bn Ahmad babban saktaren kungiyar OCI da farko yayi alawadai da matakin da shugaban Amurka ya dauka na ayyana birnin Qudus a matsayin hedkwatar HKI, tare da bayar da umarni da meda ofishin jakadancin kasar sa zuwa birnin Qudus.

Bn Ahmad ya ce wannan mataki ya sabawa dokokin kasa da kasa, da kuma sanarwa MDD, kuma hakan ya fita daga cikin kudirin kasa da kasa na hana canza yanayin Qudus.

Sakatare janar na Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) ya bukaci Kasahen Duniya da su amince da kasar Palastinu a hukumce tare da bayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin kasar Palastinu, wanda hakan shi zai kawo karshen wannan takaddama da ake yi tsakanin al'ummar Palastinu da Sahayuna.

3672464

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: