IQNA

22:32 - December 23, 2017
Lambar Labari: 3482227
Bangaren kasa da kasa, an shiryawa mabiya addinin kirista walimar cin abincin kirsimati a babban masallacin birnin Cape Town na Afirka ta kudu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na iol ya bayar da rahoton cewa, a yau Asabar an shiryawa mabiya addinin kirista walimar cin abincin kirsimati a babban masallacin birnin Cape Town na Afirka ta kudu, domin karfafa alaka a tsakanin mabiya addinin kiristanci da musulunci.

Wannan dais hi ne karo na uku a jere da mabiya addinin musunci suke gayyatar mabiya addnin kirista zuwa cin abinci a wannan masallaci a lokacin da ake gudanar da bukukuwan kirsimati.

Jamila Abrahamis day ace daga cikin masu kula da lamarin wannan masalaci ta bayyana cewa, babbar manufarsu ta yin hakan ita ce kara tabbatar da zumunci da fahimtar juna da girmama juna a tsakanin musulmi da kirista.

Ta ci gaba da cewa, musulmi da kirista dukkaninsu suna kaunar zaman lafiya da juna, domin shi ne abin da addinan guda biyu suke koyarwa.

Baya ga taron cin abinci da aka shirya ma kiristoci a wannan masallaci, an bayar da kyautuka namusamman gare su, musamman ma ga kanan yara wadanda suka halarci wurin.

Taron ya gudana cikin farin ciki da murna da nuna kaunar juna tsakanin musulmi da kirista.

3675204

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: