IQNA

Za A Girmama Wadanda Suka Halarci Gasar Kur’ani Ta Oman

23:34 - December 24, 2017
Lambar Labari: 3482230
Bangaren kasa da kasa, za a girmama wadanda suka halarci gasar kur’ani mai tsark ta sarki Qabus a kasar Oman.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, yanzu haka ana girmama wadanda suka halarci gasar kur’ani mai tsark ta sarki Qabus a kasar Oman bayan kammala wannan gasa a garin Sahar.

Sheikh Abdullah bin Muhammad Salimi minister mai kula da harkokin addini a kasar yana daga cikin wadanda za su halarci wannan taro, tare da wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin kasar.

Wannan gasa dai ta hada bangarorin harda da kuma ylawa, daga ciki akwai hardar juzui 24, da kuma juzi 18, sai juzi 12, da kuma juzui 6 da kuma juzui biyu.

Daga cikin wadanda suka shiga wannan gasar kuma suka nuna kwazo akwai wani mai fama da larura, wanda yana daya daga cikin wadanda za a grmama da manyan kyautuka na sarkin kasar.

Babbar cibiyar kula da harkokin al’adun muslunci ta sarki Qabus na kasar Oman dai ita ce ta dauki nauyin shirya wannan gasa da kuma daukar nauyinta.

3675644

 

 

 

captcha