Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, A zantawarsa da tashar talabijin ta Al-mihwar a daren jiya a birnin Alkahira na kasar Masar, Sheikh Abdulmun'im Fu'ad daya daga cikin manyan malaman cibiyar Azhar ya bayyana cewa, kamar yadda masallaci yake a matsayin wuri mai tsarki ga muuslmi, haka majami'a take a wurin mabiya addinin kirista.
Shehin malamin ya kara da cewa, 'yan ta'adda da suke kaddamar da hare-hare a kan wuraren ibada na mabiya addinin kirista, ba suna wakiltar musulmi ko addinin muslunci ba ne, domin kuwa musulunci ya koyar da musulmi girmama dan adam da mahangarsa, ballantana mabiya addinin kirista wadanda suke zaune a cikin aminci a tsakanin al'ummar musulmi.
Daga karshe malamin ya yi kira da a bayar da muhimmanci wajen yaki da akidar ta'addanci ta hanyar ilmantarwa, kamar yadda ake yaki da ita ta hanyar yin amfani da karfin makami da sauran dabaru na tsaro.