Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na post cewa, a jiya a birnin Berlin na kasar Jamus aka gudanar da tarukan tunawa da cikar shekaru biyu da shahadar sheikh Nimr babban malamin addini a kasar Saudiyya wanda masarautar kasar ta kashe ta hanyar fille masa kai.
Yusuf Muhafazah shi ne babban sakatare cibiyar kare hakkin bil adama da da dimukradiyya ta mabiya addinin muslunci mazauna kasar Jamus, ya bayyana cewa sun shirya wannan taron ne domin tunawa da wannan babban malami wanda azzaluman mahukunta 'yan kama karya da ke rike da madafun iko Saudiyya suka kashe.
Ya ce hakika kisan Sheikh Nimr ya tabbatar da irin tsoron da ke cikin zukatan sarakunan kama karya na Saudiyya, ta yadda za su kashe mutumin da babu komai a hannunsa sai carbi, saboda kawai suna jin tsoron kalamansa na gaskiya, da ke kiransu da su yi adalci su daina zalunci, su tuna haduwarsu da Allah.
A ranar daya ga watan janairun shekara ta 2016 ce mahukuntan kama karya na kasar saudiyya suka sare kan sheikh Nimr da takobi, ba tare da bayyana wani dalili ba na yin hakan.