IQNA

Kasasshen Larabawa Za Su Yi zama A Jordan Kan Quds

23:57 - January 04, 2018
Lambar Labari: 3482268
Bangaren kasa da kasa, kasashen larabawa za su gudanar da wani zama a kasar Jodan domin tattauna batun Quds.

 

Kamfanin dilancin labara iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na jaridar Al-gad ta kasar Jordan ya habarta cewa, a ranar Asabar mai zuwa ministocin wasu kasashen larabawa za su gudanar da wani zama a kasar Jodan domin tattauna batun Quds da kuma halin da ake cikin bayan sanarwar Trump.

Baya ga shugaban kungiyar kasashen larabawa, ministocin harkokin wajen kasashe Masar, Palastinu, Jordan, Saudiyya, Morocco, UAE duk za su halaci zaman.

Tun bayan da shugaban kasar Amurka ya sanar da birnin Quds a a matsayin fadar mulkin haramtacciyar gwamnatin yahudawan Isra’ila, al’ummomin muuslmi da na larabawa suke nuna rashin yardarsu da hakan.

Wannan mataki na Trump ya zo a daida lokacin da wasu daga cikin kasashen larabawa suke kulla kawance da haramtacciyar kasar Isra’ila da suka hada har da Saudiyya, domin su hada kai wajen cutar da Iran.

Al’ummomin duniya sun nuna rashin amincewarsu da wannan mataki na Amurka, inda a majalisar dinkin duniya kasashen duniya suka suka kada kuri’ar yin watsi da wanan mataki, duk kuwa da cewa dai hakan ba zai hana Amurka aiwatar da shirin nata ba.

3678829

 

 

 

captcha