Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jaridar Quds arabi ta habarta cewa, gwamnatin kasar Masar ta karyat raton da jaridar New York Time ta bayar a cikin faifan sauti da ke cewa za a gudanar da taron amincewa da Quds a matsayin birnin Isra'ila biyo bayan matakin da Trump ya dauka kan batun.
Jaridar New York Times ta rubuta cewa wani jami'in 'yan sanda na kasar Masar mai suna Asharaf Khuli shi ne ya bayar da labara kan batun, wanda kuma bida dogaro da abin da ya fada ta bayar da rahoton ta.
A kwanakin baya ne dai shugaban Amurka ya sanar da cewa ya amince da kudirin da ke mayar da birnin Quds fadar mulkin haramtacciyar kasar Isra'ila a hukumance.
Wanann lamari dai yana ci gaba da fuskantar kakkausar suka daga kasashen musulmi da na larabawa da kuma kasashen duniya daban-daban, musamman ma dai masu 'yancin siyasa daga cikinsu.