IQNA

Masar Na Fuskantar Karancin mata Makaranta Kur'ani

22:12 - January 24, 2018
Lambar Labari: 3482330
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Khalid Aljundi ya bayyana cewa daya daga cikin matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu a kasar Masar ita ce karancin mata makaranta kur'ani.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na elbalad.news cewa, Sheikh Khalid Aljundi mamba a kwamitin kula da harkokin addinin muslunci a kasar Masar ya bayyana cewa, daya daga cikin manyan matsalolin da ake fuskanta a halin yanzu a kasar Masar ita ce karancin mata makaranta kur'ani da za su taimaka wajen koayr da mata.

Aljundi ya ci gaba da cewa, a wasu lokutan da suka gabata a kasarMasar, duk gidan da e wani makarancin kur’ani, iyalan wannan gidan sukan taru domin wannan makaranci daa cikinsu ya karanta musu kur’ani mai tsarki su kuma suna saurare.

Ya ce yana fatan wannan al’ada za ta dawo a kasar Masar, domin kuwa yanzu zamani ya shagaltar da mutane sun manta da irin wadannan al’adu nasu masu kyau a kasar, kamar yadda ya yi fatan ganin an samu ci gaba ta fuskar kara samun mata makaranta kur’ani.

3684565

 

captcha