Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alhadas cewa, Redhwan Jamal Umar shugaban cibiyar gyaran littafan da aka rubuta da hannu da ke karkashin masallacin Quds ya bayyana cewa, sojojin yahudawan sahyuniya sun kai farmaki a kan ginin cibiyar tare da cin zarafin ma’aikatan wurin.
Ya kara da cewa sojojin yahudawan sun yi amfani da karfi wajen lakadawa wasu daga cikin ma’aikatan cibiyar duka, da cin zarafin su ta hanyar zagi da wulakanci.
Wannan cibiyar ita ce ta farko a yankin gabas ta tsakiya wajen gudanar da irin wannan aiki na gyaran littafan da aka rubuta da hannu na addini, kamar yadda kuma ita ce ta hudu a duniya, kuma hukumar UNIcEF ta saka cibiyar a cikin wurare na tarihi.
An kafa cibiyar ne a cikin shekara ta 2008, kuma tana ci gaba da gudanar da ayyukanta.
Ko a ranakun Asabar da kuma Lahadi yahudawan sahyuniya mas tsatsauran ra’ayi sun kai farmaki a masallacin Quds mai alfarma.
Yahudawan sahyuniya suna kokarin ganin sun mayar da palastinawa saniyar ware a cikin birninsu na Quds.
A cikin ‘yan watannin da suka gabata ne da palastinawa suka fara yin bre na nuna rashin amincewarsu da duk wani yunkuri na mayar da birnin Quds babban birnin yahuadawa.