Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Wannan baje kolin dai a kan shirya shi ne a karshen watan fabrairun kowace shekara, wanda kungiyar bayar da agaji da kasa da kasa wato red cross take daukar nauyin shiryawa, inda kasashen duniya kan baje kayayyakin al’adu tare da sayar da su ga masu zuwa duba wannan baje koli.
Ana yin amfani da dukkanin kudin da aka samu a wajen wannan baje koli ne domin gudanar da ayyukan agaji a kasashe da suke bukatar taimako.
Iran ta kan baje kayan da ake sana’antawa da hannu masu kima, wadanda a kan sayar da su a wurare na musamman a duniya, kuma a kan bayar da kudaden da sauran kayan ga kungiyar red cross bayan kamala baje kolin.
Sabanin sauran shekaru da suka gabata,a shekarar bana an bayar da dakuna uku ne ga kasar Iran, bias la’akari da yawan kayan da ta kawo wadanda suke jan hankulan masu ziyartar wurin, da kuma kimar da kayan ke da ita ga masu saye.