IQNA

Kotun Isra’ila Ta Sake Dage Shari’ar Shugaban Harkar Musulunci A Palastine

23:51 - February 28, 2018
Lambar Labari: 3482440
Kotun Isra’ila ta sake dage zaman shari’ar shugaban harkar musulunci a Palastine Sheikh Raid Salah zuwa na sama.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka gudamar da zaman sauraren shari’ar Sheikh Raid Salah, wanda Isra’ila ke tuhumarsa da nuna kiyayya ga yahudawa da kuma shiga jerin gwano da Palastinawa ke gudanarwa, wanda baya bisa dokar Isra’ila.

Shugabn tawagar lauyoyin da suke kare Ra’ida Salah ya bayyana cewa, sun zo da shirin kamala zaman shari’ar, bias bayan da kotun ta bayar, amma kuma an sake dage shari’ar da nufin kara kambama lamarin nasa.

Tun kimanin watanni shida da suka gabata ne jami’an tsaron Isra’ila suka kai farmaki a gidan Sheikh Ra’id sala a yankin Ummul Fahm da ke cikin yankunan palastinawa da Isra’ila ta mamaye, kuma tun a lokacin suna ci gaba da tsare shi.

3695147

 

 

 

 

captcha