IQNA

Jagoran Juyin Juya Halin Muslunci:

Ranar Da Zaku Yi Sallar Jam'i A Cikin Masallacin Quds Tana Nan Zuwa

21:00 - March 01, 2018
Lambar Labari: 3482441
Bangaren kasa da kasa, jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a lokacin da yake ganawa a yau da tawagar ministan harkokin addini na kasar Syria ya bayyana cewa, ranar da za ku salla a cikin masallacin tana kusa.

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yanar gizo na jagora ya bayar bayanin cewa, Ayatollah Sayyid Ali Khamenei a lokacin da yake ganawa a yau da tawagar ministan harkokin addini na kasar Syria ya bayyana cewa, ya zama wajibi kowa ya zama cikin shiri, domin kuwa ranar da musulmi za su shiga masallacin Quds suna masu izza ta kusa zuwa.

Jagoran ya bayyana irin matakan da ma'abota girman kai suke dauka domin rusa kasashen musulmi da tarwatsa al'ummar musulmi a matsayin yunkuri na gurgunta karfin musulmi, domin yahudawa su ci gaba da cin karensu babu babbaka.

Dangane da abin da yake faruwa a Syria kuwa, ya bayyana cewa wanann yana daga cikin irin wadannan manufofi na rusa kasashe masu 'yancin siyasa da kuma yin gwagwarmaya domin 'yanto wannan al'umma daga zalunci da danniyar masu girman kai da 'yan koransu.

Jagoran ya bayyana shugaba Bashar Assad a matsayin mutum mai juriya da tsayin daka, wanda kuma juriyarsa da tsayin dakan da ya yi, sun yi babban tasiri wajen juriyar da al'ummar Syria ke yi wajen tunkarar makircin 'yan mulkin mallaka  a kan kasarsu.

Haka nan kuma jagora ya kirayi al'ummar Syria da ma sauran dukkanin wadanda suke hankoron ganin sun kare al'ummarsu daga zaluncin manyan kasashe masu girman kai, da su zama masu imani da juriya, da fitar da rauni ko karaya daga zukatnasu, daga karshe da yardarm Allah za su yi nasara.

3682422

 

 

captcha