IQNA

'Yan Addinin Buda Sun Sake Kaddamar Da Farmaki Masallacin Musulmi A Sri Lanka

23:18 - March 25, 2018
Lambar Labari: 3482509
Bangaren kasa da kasa, rahotanni daga kasar Sri Lanka na cewa wasu 'yan addinin Buda sun kaddamar da farmaki kan daya daga cikin masallatan musulmi a yankin Digana, inda suka kona masallacin da kuma lalata kaddarorin da ke cikinsa.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, majiyoyin jami'an tsaro sun ce an yi dauki ba dadi tsakanin 'yan addinin Buda da kuma musulmi, a lokacin da musulmin suke kokarin kare masallacinsu daga farmakin 'yan Buda, lamarin da ya yi sanadiyyar jikkatar mutane da dama daga bangarorin biyu.

Tun da jimawa dai mabiya addinin Buda suna zargin cewa muuslmi suna neman su mamaye musu yanki, tare da kafa cibiyoyinsu da makarantu da kuma masallatai.

A cikin 'yan makonnin da suka gabata ma wani dan addinin Buda ya rasa ransa a wata hatsaniya tsakaninsa da sauran abokansa, amma kuma 'yan Buda sun dora alhakin mutuwarsa  akan musulmi, inda suka kona gidaje fiye da 200 mallakin muuslmi, gami da shaguna da kuma masallatai guda 11.

3701944

 

 

captcha