Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na Aljazeera ya habarta cewa, kwamitin kula da harkokin wuraren ibada na mabiya addinin kirista a Palastinu ya bayyana keta alfarmar wuraren ibada na kirista da yahudawa ke yi da cewa ba a bu ne da za a aminta da shi ba.
Bayanin ya ce yahudawa masu tsatsauran ra'ayi suna kai farmaki a kan wuraren ibadar kiristoci tare da samun kariya daga jami'an tsaron Isra'ila a lokacin da suka yin wannan ta'annuti.
Kwamitin kula da wuraren ibadar kiristoci na Palastinu ya ce Isra'ila ba ta yin aiki da ko daya daga cikin yarjeniyoyi da kaidoji na mutunta wuraren ibada na wasu addinai, wanda hakan ya saba wa dukkanin dokoki na duniya.
Daga karshe kwamitin ya bukaci bangarori na kasa da kasa da su dauki matakan matsa lamba kan gwamnatin yahudawan Isra'ila da ta yi aiki da doka wajen mutunta wurare na ibada.