Kamfanin dillancin labara iqna ya habata cewa, shafin jaridar Quds arabi ya habarta cewa, a yau dubban Palastinawa suka gudanar da gangamin ranar kasa karo na arba’in da biyu domin tunawa da ranar da haramtacciyar kasar sra’ila ta mamaye musu yankunan noma.
Wannan jerin gwano ya samu karbuwa a yankunan palastinu, kuma ana gudanar da shi a kowace shekara, domin nuna rashin amincewa da mamayar yankunan palastinawa da kuma, jaddada cewa palastinawan da aka kora za su dawo.
Dakarun sojojin yahudawa sun yi amfani da karfi domin tarwatsa wannan babban gangami da jerin gwanoa Gaza, inda suka yi ta antaya hayaki mai sanya hawaye da kuma harsasan bindiga masu rai, lamarin da ya yi sanadiyyar yin shahadar wasu da kuma jikkata wasu daruwa.
A ranar 30 ga watan Maris na shekara ta 1976 yahudawan sahyuniya suka kwace yankunan palastinawa da suka hada da gidaje da filaye da gonakin noma masu tarin yawa, lamarin da yasa masu wuraren suka yi bore har aka kasha 6 daga cikinsu, kuma ana tunawa da wannan rana a kowace shekara.