IQNA

An Fara Gudanar Da Wani Shiri Na Horar Da Ladanai A Tunisia

23:45 - April 10, 2018
Lambar Labari: 3482556
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani shiri nahorar da ladanai masu kiran salla a kasar Tunisia.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, shafin tashar France24 ya bayar da rahoton cewa, wannans hiri na daga cikin abubuwan da aka bullo da su da nufin kara habbaka lamarin addini a tsakanin al'umma.

Babbar manufar hakan ita ce samar da tsari a cikin lamarin masallatai musamman ma abin da ya shafi kiran salla, wanda yake da matukar muhimmanci a cikin lamarin salla da kuma abin da yashafi masallatai.

Bisa la'akari da cewa akasarin masallatai a kasar Tunsia suna bin tsari irin na gargajiya ne wajen gudanar da lamrinsu, wannan ya sanya mahukunta musamman a bangaren kula da harkokin addini, suna ta hankoron ganin cewa an tafi da zamani a bangaren addini a kasar.

Da dama daga cikin ladanan da suke shiga shirin dai sun nuna gamsuwarsu da yadda ake bas u horo kan yadda ake yin kiran salla da kuma yadda za a yi yadda zai ja hankulan jama'a domin zuwa ga salla.

3704479

 

 

 

 

 

 

 

captcha