Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na jaridar Alsabah cewa, wannan gasa an fara ta ne tun a ranar jiya Laraba.
Gasar tana samun halartar wakilai daga kasashen duniya daban-daban da suka hada da Iraki, Lebanon, Somalia, Jordan, Morocco, Yemen, Palastinu, Saudiyya, Masar, Syria, Chadi da Jibouti, wadanda adadinsu ya kai 112.
Za a kamala gasar ne a cikin mako mai kamawa, inda za a gudanar da taron karshe na rufe gasar tare da sanar da sunayen wadanda suka lashe gasar a dukkanin bangarorin da aka gudanar da ita.