Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai almotawaset.com ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da cibiyar ta Azhar ta fitar, ta bayyana wannan kira da wadannan fitattun Faransawa suka yi da cewa ya tabbatar da jahilcinsu a kan kur'ani mai tsarki.
Kakakin cibiyar Azahar Abbas Shoman ya bayyana cewa, wadanda suka yi wannan kira sun yi shi ne bisa zargin cewa wasu ayoyin kur'ani suna yin umarni da kisan jama'a ba tare da wani dalili ba, ya ce kur'ani mai tsarki yana kira ne zuwa ga kare rayuwar bil adama da mutunta, ba shekar da jinin dan adama.
Dangane da ayoyin jihadi kuwa, sun zo ne a matsayin kira zuwa ga kare kai, daga wadanda suka yi shishigi a kan musulmi, kuma shi ma bisa sharudda, kamar yadda ya kirayi masu irin wannan tunani da su koma zuwa ga littafan tafsiri na musulmi domin samun bayani kan ayoyin da suke magana a kansu.
Daga cikin fitattun mutanen da suka yi wannan kira har da tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy da kuma wasu fitattun 'yan siyasa da marubuta.