Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga reshensa na Razavi cewa, a lokacin rufe gasar karatun kur'ani mai tsarki wakilin kasar Ivory Coast Khali Sangara ya gabatar da kira'a ta tartili a jiya Litinin a lokacin rufe taron gasar kur'ani ta duniya ta daliban jami'a a birnin Masshhad na kasar Iran kamar yadda za a saurara.