IQNA

23:16 - May 03, 2018
Lambar Labari: 3482629
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Masar ta girke sojoji da kayan yaki a kan iyakokin kasar da yankin zirin Gaza.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Russia Today cewa, gwamnatin kasar Masar ta girke sojoji da kayan yaki a kan iyakokin kasar da yankin zirin Gaza da nufin kaddamar da farmaki kan ‘yan ta’adda domin murkushe su.

Haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da yahudawa mazauna yankunan palastinawa da ta mamaye, kan cewa mai yiwuwa a cikin ‘yan kwanakin nan su ji karar harbe-harben bindigogi da tankokin yaki.

Tun a lokutan baya ne dai kasar Masar ta sanar da kaddamar da yaki a kan ‘yan ta’addan takfiriyya da suka kafa tunga a cikin yankunan tsibirin Sinai, inda suke kai hare-hare a cikin kasar ta Masar.

3711123

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، palastinawa ، Masar ، bindigogi ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: