IQNA

23:50 - May 11, 2018
Lambar Labari: 3482648
Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da zaman taro na shekara-shekara kan harkokin tattalin arziki tsakanin Rasha da kasashen musulmi, taron da ke samun halartar wakilai daga kasashe 50 na duniya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa tashar talabijin ta Russia today ta bayar da rahoton cewa, kimanin mutane 3000 ne suke halartar taron a kasar Rasha, da suka hada da masana kan harkokin tattalin arziki, da manyan jami’ai a bangarori na harkokin tattalin arziki da kasuwanci.

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi lalae maharbin ga dukkanin mahalrta taron, ya kuma jaddada matsayin Rasha na kokarin ganin an ci gaba da samun kyakkyawar alaka tsakanin Rasha da sauran bangarori na duniyar musulmi a dukkanin bangarori, ba kawai a bangaren tattalin arziki da kasuwanci ba, har ma da sauran bangarori na al’adu da ilimi da sauransu.

Putin ya ce Rasha na da burin ganin an samu fahimtar juna da adalci tsakanin al’ummomin duniya, kuma za ta ci gaba da kokari da kuma sadaukarwa a kan hakan.

3713171

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، Rasha ، duniyar musulmi ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: