IQNA

23:55 - May 11, 2018
Lambar Labari: 3482649
Rundunar sojin kasar Iraki ta sanar da rusa wasu manyan wuraren buyar ‘yan ta’addan Daesh a cikin lardin Samirra da ke arewacin kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, kakakin rundunar sojin Iran Yahya Rasul ya sanar da cewa, sun fara kaddamar da farmakin ne a yankunan Pishgan da Tal Zahab a cikin lardin Samirra.

Ya ce sun samu nasarar rusa wasu muhimman wuraren buyar ‘yan ta’adda guda biyu da suke a wurin, kuma an kashe daya daga cikin ‘yan ta’addan, yayin sauran kuma suka mika kansu.

Wannan farmaki dai ya zo ne sakamakon hare-haren baya-bayan nan da ‘yan ta’addan Daesh suka kaddamar a wasu yankuna na Iraki, kamar yadda kuma ake zaton cewa ‘yan ta’addan za su zafafa hare-harensu a cikin ‘yan kwanakin nan domin kawo cikas ga zaben da za a gudanar a kasar.

3713142

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، daesh ، Iraki ، farmaki ، Samirra ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: