IQNA

23:56 - May 15, 2018
Lambar Labari: 3482662
Bangaren kasa da kasa, an gudanar dabikin yaye wasu daliban kur’ani su 200 a  wata bababr cibiyar koyar da karatun kur’ani a kasar Mauritaniya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na Siraj cewa, a jiya an gudanar dabikin yaye wasu daliban kur’ani wata bababr cibiyar koyar da karatun kur’ani a kasar Mauritaniya.

Sheikh Abdulrahman Wuld Haden shugaban bangaren zartawa na cibiyar ya bayyana cewa, kimanin sekaru goma sha daya kenan da kafa wannan cibiya, amma ya zuwa yanzu ta samu gagarumin ci gaba wajen koyar da dubban daibai.

Ya ci gaba da cewa wannan cibiya  yanzu tana da rassa guda uku, kuma akwai dalibai fiye da 3000 da suke karatu karkashin wannan cibiya  a halin yanzu.

Ya ce daga cikin ci gaban da cibiyar ta samu ne a yanzu aka yaye dalibai 200 da suka hardace kur’ani mai tsarki, kuma 50 daga cikinsu mata ne.

Cibiyar dai tana da babban ofishinta ne a brnin Nuwakshout fadar mulkin kasar ta Mauritaniya, kuma a shekara mai zuwa ana sa ran zata yaye dalibai 600 da za su kammala harda.

3714856

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: