IQNA

23:47 - May 16, 2018
Lambar Labari: 3482663
Bangaren kasa da kasa, an girmama adanda ska halarci gasar kur’ani ta makafi a kasar Mauritania.

Kamfanin dillancin labaran ina ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na akhbar.info cewa, a jiya ne aka gudanar da taron rufe gasar makafi ta kasar Mauritaniya tare da halatar jami’ai daga cibiyar kula da nakasassu ta kasar.

Sheikh Muhammad Hassan Wuld Aluddu shi ne shugaban kula da cibiyoyin bayar da agaji da taimako ga nakasassu ta kasar Mauritaniya, shi ne kuma ya mika kyautuka ga wadanda suka hakarci gasar.

Wannan cibiya dai tana samun dauki da taimako daga kasashen larabawa, inda ae bayar da ilimi kyauta ga masu fama da nakasa, da kuma daukar nauyinsu a kan wasu lamurra da suka shafi rayuwarsu.

Baya ga kyautuka da aka bayar ga dukkanin wadanda suka halarci gasar, an bayar da wasu kyautuka na musamman ga wadanda suka nuna kwazo.

3714613

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، kyautuka ، halarci ، Mauritania ، ilimi ، IQNA
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: